Kimanin Mutane 100 ne ake zaton mutuwar su bayan da wuta ta tashi jim kadan da baduwar tankar man fetur a Naija

Daga wakilin mu:

Rahotanni daga kan hanyar Kaduna zuwa Abuja na cewa a kimanin mutane 100 ne ake zaton mutuwar su a yayinda suke kwasar man fetur din wata motar tanka data fadi.

Lamarin ya faru ne a garin Dikko dake karamar hukumar Gurara a jihar Naija.

Har zuwa yanzu Kuma ba’a tantance mutanan da suka jikkata ba.

Bayanai sun ce wutar ta kama ne lokacin da mutane suka hanzarta zuwa domin kwasar man fetur din da yake kwarara a kasa ,daga nan ne wutar ta tashi.

Shaidun gani da ido sun shaida cewa anga gawarwakin mutane sun Kone kurmusu a yayinda ake ta kokarin kashe wutar.

Labarin ya haifar da cunkoson ababan hawa na tsawon lokaci.

Idan ba’a manta ba ko a watan octoban shekara 2024 da ta gabata saida aka samu rasa rayukan mutane 170 a dalilin yadda mutanan  sukaje kwasar man fetur din da yake kwarara a kasa a garin Majiya dake karamar hukumar Taura a jihar Jigawa lokacin da tankar man fetur din ta fadi.

A wasu lokuta, akasarin wadanda abin ke rutsawa da su, mutane ne da ke taruwa a kusa da motar dakon man domin dibar mai daga cikin tankar kafin wani mummunan abu ya afku kamar yadda a yanzu ta faru a Jigawa da Naija.

Post a Comment

0 Comments