Gwamnatin Kano Ta Gudanar Da Rangadin Duba Filin Idi Da Wasu Mahimman Gurare.


A kokarinta naci gaba da tabbatar da ingantacciyar tsafta da yanayi Mai kyau a cikin birnin kano, a yau Gwamnatin Kano ta gudanar da wani rangadi a filin Idi dake Kofar mata domin duba yanayin tsaftarsa da wasu muhimman gurare.
Kwamishinan Ma'aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayi na jihar kano Dr Dahiru Mohammad Hashim ne ya jagoranci rangadin a wani bangare na gudanar da aikin tsaftace muhalli na karshen wata na ma'aikatun Gwamnati da Kasuwanni da Tashoshin mota.

Kwamishinan Wanda mukaddashin Secretary Ma'aikatar Dr. Abdulhamid Bala ya wakilta ya bayyana gamsuwarsa da yanayi da Filin Idi yake ciki. Haka kuma tawagar ta shiyarci yakasai yandabino gurin da ake Tara shara da Durimin zungura da Durimin iya da Old library jikin katangar gidan Sarki da NA park harma da Kofar kudu wato titin gidan Sarki, domin duba yanayin da aikin kwashe shara da tsaftace tituna yake gudana a jihar kano, duk a wani bangaren  na aikin tsaftace muhalli na karshen wata na ma'aikatu da sauran guraren taruwar jama'a.

Kwamishinan ya bayyana gamsuwarsa tare da shan alwashin duk inda ya rage sauran aiki za'a tabbatar da kammala shi kafin ranar sallah domin baiwa jama'a damar zirga-zirga cikin yanayi Mai kyau.

Dr. Hashim ya bukaci jama'a dasu Kara baiwa gwamnati goyon baya wajen kiyayewa tare da bin ka'idar dokokin Muhalli don kaucewa gurbacewar Muhallin, musamman a wannan lokaci na bukukuwan sallah.

Haka kuma yayi fatan alheri tare da addu'a Allah ya karbi ibadum da aka gudanar a cikin wannan wata Mai alfarma tare da fatan Allah ya baiwa Jihar kano da Kasa Nigeriya zamani lafiya da karewar arziki.

Ismail Garba Gwammaja,
Diraktan wayar da kan Jama'a 
Ma'aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayi, jihar kano.

Post a Comment

0 Comments