A kokarinta na tabbatar da ingantacen Muhalli Mai tsafta a duk fadin Kano da kewaye, Gwamnatin Jihar Kano ta Samar da ingantacciyar dokar Kare Muhalli daga gurbacewa da nufin kawo daidaito da inganta lafiya Muhallin.
Kwamishinan ma'aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayi na Jihar Kano Dr. Dahiru M. Hashim ne ya sanar da hakan lokacin da yake gabatar da kundin dokar ga sakataren gwamnatin Jihar Kano Alh. Umar Faruk Ibrahim a ofishinsa.
"Kwamishinan yace matukar gwamnatin Kano ta amince da wannan dokoki to babu shakka zasu kawo daidaito da Kuma Kare Muhalli daga gurbacewa," inji Kwamishinan.
Haka Kuma yace da zarar gwamnatin ta gamsu da wadan nan dokokin ma'aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayin zata dukufa wajen fadakarwa tare da wayar da kan jama'a game da wannan sabuwar doka na tsawon makonni takwas domin Kowa yasan da zuwan ta da Kuma irin abubuwan data Ke dauke dashi.
Dr. Hashim Wanda ya bayyana burin sa na samar da isasshen kofin wannan doka cikin harshen Hausa da Turanci nan bada dadewa ba domin al umma su fahimci tanade - tanaden dake cikin wannan doka Kamar yadda ya kamata.
Da yake nasa jawabin sakataren gwamnatin Jihar Kano Alh. Umar Faruk Ibrahim ya bayyana gamsuwar sa game da wannan ci gaba da aka Samar Sai dai yayi tsokaci game da wasu sassa na wannan dokar Inda ya bada shawara akan abin daya dace domin tabbatar da adalci da Kuma daidaito a Ko wane bangare. Haka Kuma sakataren gwamnatin Jihar ya bada tabbacin baiwa kunshin wannan doka duk kannin goyon bayan daya dace domin cimma bukatar da ake da ita.
*Signed:
Ismail Garba Gwammaja,
Directan Wayar da kan jama'a na ma'aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayin ta Jihar Kano.*
0 Comments