Yanzu- Yanzu daya daga cikin Kwamishinonin Gwamnatin Kano ya sauka daga kan kujerar sa*

Kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida Manjo Janaral Muhammad Inuwa Idiris mai ritaya ya sauka daga mukamin sa na Kwamishina ba tare da wani bata lokaci ba .

Wata takarda da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano  Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar yace gwamna Yusuf ya kadu da ajiye aikin da kwamishinan yayi

Ya kuma mika sakon godiya sosai abisa gudun mowar da ya bayar.

Tuni gwamna Yusuf ya karbi takardar ajiye aikin na kwamishinan tsaron nan take.

Mujallar Optical Hausa  ta rawaito cewa kwamishinan bai bayyana dalilansa na ajiye aikin ba

Post a Comment

0 Comments