An yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta amince da daga likafar Gandun Dajin Falgore zuwa Gandun Daji na Kasa.
Mambobin Kungiyar Masu Kishin Jihar Kano wato Kano State Citizens Concerned Forum ne suka yi wannan kira ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Lahadin nan.
'Yan kungiyar sun yi kira ga Gwamnan Jiha, Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta amincewa da wannan abu na cigaba saboda dumbin alfanun da hakan ke da shi ga jihar nan da ma al'ummarta.
A cewar kungiyar d'aga likafar Gandun Dajin na Falgore ta hanyar danka shi a hannun Hukumar da ke Kula da Gandun Daji ta Kasa NPS zai ba da damar samun aikin yi a gwamnatin tarayya da inganta noman rani a yankin Kano ta Kudu.
Sauran alfanun da jihar nan za ta ci gajiyarsu sun hada da inganta harkar tsaro da bunkasa yawon bude ido da kuma kare tsire-tsire da dabbobi da ke rayuwa a Dajin na Falgore.
Daga nan sai suka bayyana taikaicinsu dangane da halin da Dajin ke ciki sakamakon yawan sare bishiyoyi da wasu marasa kishi ke yi, wanda hakan ya sa wasu nau'in bishiyoyi suka 'kare gaba daya, a yayin da sauran bishiyu da dama ke fuskantar barazanar 'bacewa d'ungurungun.
0 Comments