Gwamnatin jahar Kano ta bayyana gamsuwarta game da yadda hujun shanu na bana Ke gudana.

*

Mai tace labaran:Ismail Garba Gwammaja 

Mataimakin Gwamnan jahar Kano Kuma Kwamishinan ma aikatar kananan hukumomi da masarautu Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo ne ya bayyana hakan lokacin da yace duba yadda aikin Ke gudana a kananan hukumomi 44 dake fadin jahar nan.

Mataimakin Gwamnan Wanda Director Kula da harkokin noma na ma aikatar yake wakilta Alh. Ibrahim Lawan ya bayyana gamsuwarsa game da yadda yaga aikin na tafiya a wasu cibiyoyi dake Yahaya Gusau da Malafa da Kofar Wambai dake karamar hukumar birni.

Babban Jami'in Hulda da jama'a na maaikatar kananan hukumomi ta masarautu ta jahar Kano Malan Dahiru Lawan K/Wambai ne ya turo mana da labarin.

Mataimakin Gwamnan yace wannan hujun shanu abu ne da gwamnati take gudanar dashi Ko Wace shekara, karkashin maaikatar kananan hukumomi ta Jaha tare da hadin gwiwar maaikatar Gona da albarkatun kasa ta jaha tare da tallafin hukumar dake tallafa harkokin aikin noma da ci gaban kasa (KSADP) da nufin Samar da dadbobi masu koshin lafiya ga al- ummar jahar nan.


Comrade Abdulsalam ya bukaci duk kannin makiyaya da sauran jama'a dasu amfani da wannan dama don Mika dabbobin su wajen wannan allura domin Kare su daga mamayar cututtukan da Kan addabi dabbobi.

Haka Kuma shugaban sashen Gona na karamar hukumar birni, Alh. Sulaiman Isyaku Dakata shine ya zagaya da wannan tawaga sassan da ake gudanar da wannan aikin a karamar hukumar birni.

Post a Comment

0 Comments