*A Taron Nuna Amfanin Gona Na Kasa da ya Gudana a Jahar Nasarawa,
_Daga Maitace Labarai:_
Jami'in hulda da jama'a na maaikatar Kananan hukumomi Malan Dahiru Lawan K/Wambai ne ya turo mana da labarin Kamar haka.
Kananan Hukumomin da suka Samu Saka Makon sun hada da Karamar hukumar Birni da Dawakin Tofa da Bagwai, Wanda suka samu matsayi na farko dana biyu dana Uku, a yayin kammala bikin baje Kayan noma na kasa wanda ya gudana a jahar ta Nasarawa.
Babban jami'in shirye-shirye na cibiyar samar da kayan amfani ta kasa Mr. Samuel Ingandu, ne ya sanar da saka makon lokacin da yake mika takardar halartar taron da kuma takardar karramawa ga Kananan hukumomin da suka fi kwazo.
Lokacin da yake karbar Saka Makon amadadin mataimakin Gwamna kuma Kwamishinan Kananan Hukumomin da Kula da masarautu na Jahar Kano, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo Wanda Directan Kula da harkokin Gona na maaikatar Alh. Ibrahim Lawan ya wakilta ya bayyana farin cikin sa game da wannan gagarimar nasara da Kananan Hukumomin suka samu, Wanda yace abin alfahari ne da fatan zasu rike wannan kambun a shaikara Mai zuwa
Ana sa jawabin shugaban kungiyar tsangayar Directocin Kula da aikin gona na Jahar Kano Kuma Directan sashen Kula da aikin gona na Karamar hukumar Birni Alh. Sulaiman Isyaku Dakata bayyana farin cikin sa yayi da samun wannan nasara tare da yabawa gwamnatin Kano saboda daukar nauyin wannan hidima zuwa jahar Nasarawa tare da alkawarin cigaba da samun irin wannan nasara a nan gaba.
0 Comments