*Kwamishinan Ma'aikatar Muhalli da kula da Sauyin yanayi na Jahar Kano Hon. Nasiru Garo, ya bayyana rashin gamsuwarsa ga yanayin da wasu bandaku nan ma'aikatun gwamnati ke ciki.*

Daga Editor:

Kwamishinan maaikatar muhalli da Sauyin yanayi na Jahar Kano Hon. Nasiru Garo ya bayyana rashin gamsuwarsa ga tsaftar wasu daga cikin bandakuna na ma'aikatun gwamnati.Kwamishinan Wanda ya bayyana rashin gamsuwarsa a yau yayin da yake duba Shirin aikin tsaftar muhalli na Juma'ar karshen ko wane wata Wanda ma'aikatu da sauran guraren hada - hadar jama'a ke gudanarwa a duk Juma'ar karshen wata.

Garo Wanda yau ya ziyar ci  manyan ma'aikatun gwamnatin dake harabar Sekatariyar Audu Bako, Wanda ya fara da hukumar kula da daukar ma'aikata ta jahar Kano wato CSC da Offishin Shugaban Ma'aikata Head of Service da Ma'aikatar yada labarai da al-amuran cikin gida sai Offishin Mai binciken kudi  wato Auditor General.
Kwamishinan ya bukaci ma'aikatan hukumar kula da daukar Ma'aikata wato CSC da na Offishin Shugaban Ma'aikata dasu Samar da ruwa a bandakunan su, tare da bada kula ta musamman ga yanayin tsaftar bandakunan don inganta walwalar ma'aikatan da kare su daga kamuwa da cututtuka, haka Kuma ya yaba ga yanayin tsaftar harabar ma'aikatun guda biyu.

Da yake sharhi ga Ma'aikatar yada labarai da Offishin Mai binciken kudi na Jaha, Kwamishinan ya yaba musu bisa tsaftace muhallin nasu musamman bandakuna da harabar ma'aikatun nasu, ya shawarcesu dasu Kara sa ido sosai a bangaren makewayi don kaucewa kamuwa da cututtuka.

Kwamishina Nasiru Garo, ya jadda da kudirin gwamnati na ci gaba da bibiya domin tabbatar da ingantaccen muhalli a duk kannin manya da kananan ma'aikatun gwamnati da kasuwanni da tashoshin mota harma da kamfanoni masu zaman kansu, da nufin inganta walwala da tsafta a jahar Kano.

Da yake jawabi a mamadin ma'aikatun gwamnati Babban Mai binciken kudi na Jahar Kano, wato Auditor General Malan Ismail Musa ya bayyana farin cikin sa ga wannan ziyara da tawagar Kwamishinan suka kawo inda yake tabbas an zaburar dasu wajen inganta tsaftar muhallin nasu a duk kannin harabar Ma'aikatar su, don inganta yanayin aiki na yau da kullum har ma da walwala ma'aikatan su.

Post a Comment

0 Comments