Taron Kungiyar Tsofaffin Daliban Secondary School Gwarzo.*



 *_Kungiyar ta Jadda da Kudirinta naci Gaba da Inganta yanayin Koyo da Koyarwa a Makaranta._*

 *Editor* :

Shugaban Kungiyar tsofaffin daliban Sakandiren garin Gwarzo na kasa Alh Ahmad Ado Kibiya ne ya furta hakan lokacin taron Kungiyar na kasa karo na biyar Wanda aka gudanar a babban dakin taro dake harabar gidan zoo cikin birnin Kano.

Alh. Ado Kibiya Wanda ya bayyana irin nasarorin da 'ya'yan wannan Kungiyar suka cimma daga dan lokacin da aka sake farfado da Kungiyar bayan da aka yi zaben sabbin shuwagabannin, Kungiyar ta cimma nasarar gyara wasu daga cikin bandakunan makarantar da Samar da kujeru da Samar da ruwa da Kuma gyaran hostel na daliban da sauran su.

Shugaban yace a halin yanzu haka motocin makarantar guda biyu wato School buses, Sun gaza haka Kuma Dining hall na daliban Shima Yana bukatar kulawar gaggawa da sauran matsaloli dake bukatar kulawa ta musamman, inda ya godewa tsoffin daliban saboda gudummawar da suke bayarwa harma da tallafawar da suka Yi wajen tabbatar da nasarar wannan taron da aka gudanar duk da karancin lokacin da aka bayar da fatan Allah ya sakawa kowa da alheri.

Shima da yake nasa jawabin na bude taron tun da farko  Shugaban taron Kuma Shugaban kwamitin amintattu na Kungiyar Alh. Bala Umar yayi fatan alheri tare da jan hankalin  tsofaffin daliban dasu Kara dagewa wajen hada hannu da nufin ciyar da ilmi gaba.
Babban mai jawabi a taron Kuma tsohon Shugaban makarantar Alh. Muhammad Tuta Ahmad, ya bukaci gwamnati data sake jawo yan kishin kasa da kungiyoyi dama dai dai kun jama'a yan kishin kasa dasu shigo cikin harkar ilmi don Samun ingantacciyar mako ma.

Sauran wadan da sukai jawabi a taron akwai Farfesa Nasir Tukur Dabo da Alh. Abubakar Hashim Beli.

Daga bisa ni  Kuma an gabatar da rahoton kudi na Kungiyar tare da gabatar da addu'oi na musamman ga wasu daga cikin 'ya'yan yan Kungiyar da suka rigamu gidan gaskiya.

Post a Comment

0 Comments