*An bukaci matasa dasu Kara rungumar karatun Al-Qur'ani a matsayin hanyar tsira duniya da lahira.*


 *Editor:*

Mai martaba Sarkin Karaye Alh. Dr. Abubakar Ibrahim ll ne  yayi wannan Kiran lokacin daya ke jawabi a gurin saukar karatun Al-Qur'ani na yara (46) na makarantar Ma'ahad Sani Yahaya Littahfizil Qur'an dake karamar hukumar Nasarawa a unguwar Tudun Wada.

Sarkin Wanda Sarkin Dawakin tsakargida na masarautar Karaye Alh. Garba Ibrahim ya wakilta yace babu shakka a halin yanzu karatun Al-Qur'ani ne kadai mafita Kuma hanya daya tilo Mai shiryarwa da daukaka duniya da lahira, a don haka Sarkin yace ya zama wajibi matasan mu su Kara zage dantse wajen neman ilmin addini don saita rayuwar mu a kwakkyawan tafarki.

Ana sa jawabi Dakacin Tudun Wada Alh. Ibrahim Aliyu bayyana gamsuwarsa yayi ga yanayin Koyo da Koyarwa na wannan makaranta tare da yabawa shugabanci harma da Malaman makarantar saboda irin yadda suke rike amanar daliban su tare da basu ilmi da tarbiyya gamsasshiya da nufin samar da dalibai masu hazaka.

Da suke nasu jawaban daban - daban Dr. Muhammad Ghali Musa Shareef, babban limamin masallacin Juma'a na badawa layout da Kuma Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, Sun ja hankalin dalibai dasu zama masu yin koyi da koyarwar Al-Qur'ani da Sunnah a duk kannin al-amuran su na rayuwa baki daya don Samun tsira duniya da lahira.

Haka Kuma Sun yi tsokaci akan falalar Al-Qur'ani da mahimmancin ci gaba da karantashi bayan an haddace shi dama illar rashin bibiyar Al-Qur'ani Wanda kan iya jawo rushewar tulawar baki daya.
Ana sa bangaren Diraktan Makarantar ta Ma'ahad Sani Yahaya Littahfizil Qur'an Alh. Habibu Sani Yahaya ya yi jawabi akan kafuwar makarantar tun da farko da Kuma bayyana irin nasarorin data samu izuwa yanzu Wanda yace baza su lissafuba.

Alh. Habibu Sani ya Kuma godewa duk kannin mutanen da suke bada gudummawa wajen nasarar wannan makaranta tare da Yi musu fatan alheri.

An Kuma bada lambobin karramawa ga wasu mutum goma da suka fi hidima da wannan makaranta wajen Kara daga darajarta da martabarya Wanda ya kaita kan matsayin data ke Kai yanzu.

Sauran wadan da sukai jawabi a yayin wannan taron akwai Shugaban Kungiyar iyaye da malamai na makarantar Farfesa Muhammad Bilyaminu Ado da Malami Mai bada Darasu Malam Abdulkadir Muhammad Saleh.

Daga cikin daliban da sukai hadda Kuma sukai karatu akwai, Habiba Abdullahi Baba da Abubakar Sulaiman sai Mus'ab Abdullahi Muhammad.

Post a Comment

0 Comments