Shugaban Kasar Amurika Donald Trump ya gargadi manema labarai a Amurika akan yawan yiwa maganganunsa gurguwar fahimta Inda yace ana sauya masa zance na gaskiya a mayar dashi na karya.
Trump yace ana yiwa gwamnatinsa karya kan abinda take yi da kaso 98 cikin 100.
Shugaban na Amurika yayi wannan tsokaci ne lokacin da yake ganawa da Elon Musk mamallakin Tuwita.
Trump na maida wannan martani ne ga manema labarai a Amurika da sauran kasashen duniya bayan da ya samu labarin cewa ana yada jita jitar wai Elon Musk din ne yake juya gwamnatin Amurika saboda alakarsa da Trump.
Shugaban na Amurika na 47 ya bayyana yan Jaridar da suka hada wannan labarin a matsayin wadanda suke neman bata masa gwamnati.
Yace a tarihin siyasar Amurika babu wani Shugaba da ake juyawa magana ake kuma yada labarai marasa dadi akansa sama dashi.
Saidai Trump yace yana godiya ga Amurikawa tunda su ba marasa fahimta bane ,suna tantance gaskiya da karya.
Tun bayan rantsar da Trump a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2025 Shugaban ya sanya hannu akan wasu dokoki a kasar,kuma daga nan wasu ke ganin akwai dokokin da ba ra’ayinsa bane.
0 Comments