zamu tabbatar da mun bada aiki na dundundun ga duk dan yiwa Kasa hidima da yafi nuna kwazo - Dr. Hashim

An bukaci 'Yan yiwa Kasa hidima dasu zamo masu kwazo a wajen ayyukan su na yau da kullun, don bada gudunmawar su wajen ciyad da jihar kano gaba cikin hanzari.

Kwamishinan Ma'aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayi na jihar kano Dr Dahiru Mohammed Hashim ne ya furta hakan a yau lokacin da yake ganawa da Yan yiwa Kasa hidimar wadan da aka turasu Ma'aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayi ta jihar kano. Kwamishinan ya bayyana musu inda kowa zai gudanar da aikin sa tare da duba yiwuwar samar musu da gidajen kwana da basu alawus Mai gwabi don kyautata musu.

Dr Hashim yace a shirye Ma'aikatar sa take ta dauki mutum guda aiki da dundundun musamman ga Wanda ya nuna kwazo da gwarewa a aikin sa, ya yi musu fatan alheri tare da fatan kammala lokacin su na hidimar Kasa lafiya.

Da yake nasa  jawabin a mamadin sauran  Yan yiwa Kasa hidimar ya bayyana farin cikin su tare da godiya ga Kwamishinan saboda da wannan tagwomashi da karamcin da ya nuna musu, tare da yin alkawarin aiki tukuru don kawo ci gaba a wannan ma'aikata .

 Signed:
Ismail Garba Gwammaja 
Director Public Enlightenment,
Ministry of Environment and Climate Change, Kano State.

Post a Comment

0 Comments